in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane miliyan 1173 sun kalli bikin kade-kade da raye-raye da CMG ya gabatar
2019-02-05 19:39:49 cri
Bikin kade-kade da raye-raye da babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya gabatar jiya, don taya murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin ya kafa tarihi, inda alkaluma suka nuna cewa, gidajen telabijin 239 dake cikin kasar Sin sun watsa bikin, yayin da kafofin watsa labaru 218 dake kasashen waje, wadanda ke da huldar hadin gwiwa da CMG, suka watsa wannan biki a kasashe da yankuna 162. Ban da wannan kuma, an watsa bikin ne ta hanyoyi daban daban, wadanda suka hada da telabijin, da yanar gizo, da kuma shafunan sada zumunta. Sa'an nan yawan jama'ar da suka kalli bikin ya kai miliyan 1173, wanda ya karu da miliyan 42 bisa yawan mutanen da suka kalli bikin da aka nuna a bara. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China