Alkaluma sun nuna cewa, a bana yayin bikin bazara na shekarar 2019, kusan Sinawa fiye da miliyan 400 ne za su yi yawon shakatawa, sa'an nan miliyan 7 daga cikinsu za su tafi kasashen ketare. Mutanen da suka zo daga birane fiye da 100 na kasar Sin, za su tafi zuwa garuruwa fiye da 900 na ciki da wajen kasar Sin, domin ziyararsu ta kashe kwarkwatar ido. (Bello Wang)