in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kafa kamfanin samar da nakiya don taimakawa aikin hako ma'adanai a Zimbabwe
2019-02-01 11:10:31 cri

Nan gaba kadan kasar Sin za ta kafa wani kamfanin samar da nakiya a kasar Zimbabwe wanda zai taimkawa kasar ta kudancin Afrika a bangaren hako ma'adanai, jami'in ofishin jakadancin kasar Sin a Zimbabwe, Zhao Baogang, shi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

Jami'in ya shedawa 'yan jaridu bayan wata ganawa da shugaban kasar Emmerson Mnangagwa cewa, kamfanin samar da nakiyar zai taimakawa kasar Zimbabwe wajen bunkasa ci gaban tattalin arzikinta ta hanyar samar mata da kudaden musaya na kasashen waje.

A shekarar 2019, ana fatan za'a samu karin ayyuka a Zimbabwe. Daya daga cikinsu shi ne kamfanin samar da kujeru, tebura da gadaje, da kuma kamfanin samar da nakiyoyi karkashin hadin gwiwar Sin da Zimbabwe. Wannan za'a kaddamar da su nan ba da jimawa ba kuma zai taimakawa kasar Zimbabwe matuka musamman wajen ci gaban fannin hakar ma'adanai domin kasar ta dena shigo da nakiyoyi daga kasashen waje.

Kasar Sin ta kaddamar da ayyukan samar da kyayyakin more rayuwa na biliyoyin daloli a kasar Zimbabwe a shekarar 2018, tun bayan da ta kara daga matsayin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni na cikakkiyar abokantaka, da ingantacciyar hadin gwiwa tun a watan Afrilun shekarar da ta gabata.

Daga cikin ayyukan, sun hada da aikin samar da lantarki mai karfin mega watt 300 a Kariba, dake kudancin kasar, aikin da ya kashe dala biliyan 1.5 na fadada lantarkin a tashar Hwange Thermal, da aikin fadada filin jirgin saman kasa da kasa na Harare, da kuma gina sabuwar harabar majalisar dokokin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China