in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta alkawarta zurfafa dangantaka da sabuwar gwamnatin Zimbabwe
2017-11-30 09:26:53 cri

Kasar Sin ta bayyana fatan ta, na karfafa dadaddiyar dangantaka irin ta gargajiya dake tsakanin ta da sabuwar gwamnatin kasar Zimbabwe. Mai ba da taimako ga ministan harkokin wajen kasar Sin, kuma wakilin musamman na kasar ta Sin Chen Xiaodong ne ya bayyana hakan, yayin ganawar sa da sabon shugaban kasar ta Zimbabwe Emmerson Mnangagwa.

Mr. Chen wanda ya mika sakon taya murnar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaba Mnangagwa, ya ce Sin za ta tallafa wa ci gaban kasar Zimbabwe bisa tsari mafi dacewa da yanayin kasar. Za kuma ta karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen, ciki hadda wanda ya jibanci mataki na kasa da kasa.

Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, a nan gaba, sassan biyu sun amince da samar da wani tsari na hadin gwiwa, wanda zai tabbatar da bunkasa, tare da zurfafa hanyoyin samar da ci gaba, baya ga inganta rayuwar al'ummar Zimbabwe.

Cikin sakon na taya murnar kama aiki, shugaba Xi ya jaddada kudurin gwamnatin sa, na aiki tare da sabuwar gwamnatin Zimbabwe, a fannin bunkasa hadin gwiwar sassan biyu a bangarori daban daban, ta yadda kasashen biyu za su ci gajiya tare.

Shugaba Xi ya kuma gayyaci Mr. Mnangagwa da ya ziyarci kasar Sin a duk lokacin da ya ga ya dace, domin ci gaba da fadada zumuntar dake tsakanin sassan biyu.

A nasa martini, shugaba Mnangagwa ya ce, kasar ta Sin ce ta farko da zai ziyarta a tsakanin kasashen dake wajen nahiyar Afirka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China