in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya jagoranci bikin bude filin jirgin saman da aka gina da taimakon Sin
2016-11-21 11:10:19 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya kaddamar da bikin bude filin jiragen saman kasa da kasa na zamani na Victoria Fall da aka gina tare da taimakon kasar Sin a karshen makon da ya gabata.

Mista Mugabe ya bayyana cewa, wannan sake gyaran zai iya sauya filin jiragen saman zuwa wata cibiyar bude ido ta shiyya idan aka yi tanadi yadda ya kamata ta fuskar kasuwanci.

Kammala aikin filin jirgin ya kasance wani muhimmin mataki a cikin kokarin bunkasa kasar, tare da taimakon kasar Sin, da ya bayyana ta a matsayin wata babbar abokiyar hulda.

Kamfanin Jiangsu na kasar Sin ya gudanar da ayyukan fadada filin jirgin tun daga shekarar 2013, tare da wani rancen kudi na dalar Amurka miliyan 150 daga bankin kasuwancin kasar Sin.

A yanzu haka, filin jirgin na zamani na karbar fasinjoji miliyan 1,5 a ko wace shekara, wanda ya karu idan aka kwatanta da fasinjoji dubu 500, kuma ya kunshe da sabbin wuraren fasinjoji na zamani, da wata sabuwar tashar shige da ficen fasinjoji, da sabuwar hanyar tashi da saukar jiragen sama ta tsawon kilomita biyar, da kuma wata sabuwar cibiyar sarrafa sauka da tashin jiragen sama, da wata sabuwar tashar ma'aikatan kashe wuta da sabuwar tashar tashi da saukar fasinjoji ta cikin gida da sauransu.

Mista Mugabe ya nuna yabo ga kamfanin Sin game da yadda ya tafiyar da ayyukansa, kuma ya bayyana fatan neman taimakon wannan kamfani a cikin wasu ayyukan gine gine irin wadannan a nan gaba. Inda ya kara da cewa, Harare da sauran filayen jiragen saman kasar, ya kamata a kara fadada su da kuma kyautata su. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China