in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi alkawarin taimakawa Zimbabwe jure matsalolin tattalin arziki
2016-06-22 10:47:33 cri

Kasar Sin ta yi alkawari a ranar Talata na ci gaba da taimakawa kasar Zimbabwe domin fuskantar hamada da jure matsalolinta na tattalin arziki.

Zambabwe na dab da fadawa cikin matsalar tattalin arzki mai tsanani, dalilin tafiyar hawainiyar bunkasuwar tattalin arzki, mutuwar kamfanoni, karancin zuba jarin waje, da kuma matsalar rashin kudi mararan a cikin bankuna, lamarin da ya janyo karancin kudi mararan tun cikin watan Maris din da ya gabata.

Mataimakin ministan harkokin wajen Sin, Zhang Ming, dake ziyarar aiki a Zimbabwe, ya shaida wa 'yan jarida bayan wani taro da shugaba Robert Mugabe a birnin Harare cewa, kasar Sin ta jima tana taimakawa Zimbabwe cimma sauyin tattalin arzki domin bunkaka ci gaban tattalin arziki da na al'umma.

Mista Zhang ya kuma tabo ci gaban da aka samu wajen aiwatar da yarjeneniyoyi daban daban na dangantaka da aka rattaba tsakanin shugaba Robert Mugabe da shugaban kasar Sin Xi Jinping a shekarar 2015, daga cikinsu akwai batun gina sabuwar majalisar dokokin Zimbabwe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China