in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamandojin AU sun amince da wanzar da zaman lafiya a Somalia yayin da ake tsaka da shirin mika ragamar ayyukan tsaro
2018-04-16 09:38:04 cri

Manyan kwamandojin shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika (AMISOM) wanda ke aiki a Somalia, sun yanke shawarar ba da muhimmanci sosai ga aikin da zai ba shirin damar cimma burinsa na wanzar da zaman lafiya a kasar yayin da yake kokarin mika ragamar ayyukan ga dakarun kasar.

Wata sanarwa da shirin ya fitar jiya a Mogadishu, ta ce a karshen taron da suka yi, kwamandojin AMISON sun amince su sake nazari nasarorin da aka samu kawo yanzu ta fuskar mika ragamar aikin, domin tabbatar da tafiyar da shirin yadda ya kamata.

Mataimakin kwamandan shirin mai lura da sashen ayyuka da tsare-tsare Charles Tai Gituai, ya ce sabon shirin na bukatar saukaka hanyoyin mika nauyin tabbatar da tsaro ga dakarun Somalia, ba tare da yin barazana ga nasarorin da aka cimma ba.

Ya ce, aikinsu a bayyane yake, kuma shi ne fatattakar mayakan Al-shabaab domin taimakawa al'ummar Somalia yin rayuwa cikin kwanciyar hankali, tare da komawa ga harkokinsu na yau da kullum. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China