in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU za ta janye dakarunta daga Somaliya nan da shekarar 2018
2016-07-19 10:30:26 cri

Kungiyar tarayyar Afrika AU ta tsai da kudurin janye dakarunta daga kasar Somaliya a shekarar 2018, in ji wani babban jami'in AU.

Smail Chergui, kwamishinan AU kan zaman lafiya da tsaro, ya bayyana a ranar Litinin cewa, janye tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar AU dake kasar Somaliya (AMISOM) zai taimakawa Somaliya daukar nauyinta da kanta wajen kula da kasar.

Muna hasashen horar da samar da kayayyaki ga dakarun Somaliya kafin mu janye daga kasar, in ji mista Chergui a yayin wani taron manema labarai na kammala taron kolin AU karo na 27 a birnin Kigalin Rwanda.

Haka kuma AU na taimakawa Samaliya wajen shirya zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisu da ya kamata a gudanar kafin nan da karshen shekara, in ji jami'in.

Muna bukatar wata kasar Somaliya ta zaman lafiya dake girmama 'yancin dan adam da kuma jama'ar kasar, in ji mista Chergui, tare da jaddada cewa, taron kolin shugabannin kasashen Afrika ya kafa wani asusun musamman domin yaki da ta'addanci a nahiyar Afrika.

Wannan asusun zai samu taimakon kudi daga gwamnatocin kasashe mambobin AU, gamayyar kasa da kasa da kuma sauran abokan hulda, kuma zai fara aiki bayan an tabbatar da yadda aikinsa zai gudana.

Wannan asusun zai taiamakawa gwamnatocin Afrika mayar da martani yadda ya kamata wajen dakile karuwar ta'addanci dake haddasa mutuwar mutane da dama, in ji mista Chergui. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China