in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara karfafa matakan kare ikon mallakar fasaha
2019-02-01 10:53:43 cri

Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar cewa, kasar za ta ci gaba da daukar matakan karfafa ba da kariya ga hakkin mallakar fasahar kira, ta hanyar bin dokoki, matakan shari'a, da amfani da hukumomin tabbatar da bin doka da oda a kasar.

Kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya bayyana a taron manema labaru cewa, za'a dauki karin matakan inganta ba da kariyar ga fasahar kira, da zartar da hukunci kan dukkan wadanda aka samu da hannu wajen keta hurumin dokokin da suka shafi mallakar fasaha.

Dokar ba da kariya ga hakkin mallakar fasahar kira, wani muhimmin bangare ne na darftarin dokar zuba jarin 'yan kasuwan kasashen waje wanda za'a duba a lokacin taron shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC a watan Maris dake tafe.

Kasar Sin ta samu gagarumar nasara a bangaren ba da kariya ga fasahar kira a cikin 'yan shekarun da suka gabata, in ji Gao. Dokokin ba da kariya ga hakkin mallakar fasahar kira sun dace da tsarin dokokin kasa da kasa kuma an amince da dokokin ne karkashin kotuna na musamman da aka kafa a manyan biranen kasar Sin da suka hada da Beijing da Shanghai. Kuma gwamnatin kasar Sin tana ci gaba da yaki da laifukan satar fasaha.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China