in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan wajen Sin ya gana da shugabar Habasha
2019-01-04 19:27:33 cri

Jiya Alhamis shugabar kasar Habasha Sahle-Work Zewde ta gana da mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi a fadar shugabar kasar dake Addis Ababa, fadar mulkin kasar ta Habasha, inda shugaba Sahle-Work ta bayyana cewa, gwamnatin kasarta da fannoni daban daban na kasar suna mai da hankali matuka kan karfafa hadin gwiwa dake tsakanin Habasha da kasar Sin, haka kuma suna sa ran cewa, za a ciyar da alakar dake tsakanin sassan biyu gaba lami lafiya, kana Habasha za ta ci gaba da goyon baya da kuma shiga shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin a harkokin kasa da kasa.

A nasa bangare, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin da Habasha kasashe ne masu tasowa, ci gabansu zai taimaka ga ci gaban kasashe masu tasowa, yana fatan gwamnati da jama'ar kasar Habasha za su samo hanyar da ta dace da yanayin da kasar ke ciki yayin da take kokarin raya kasa, kasar Sin ita ma tana son kara karfafa hadin gwiwa mai dorewa tsakanin sassan biyu domin ciyar da kasar Habasha gaba da kuma inganta rayuwar al'ummar kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China