in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta samu kudin shiga dala miliyan 38 na kayayyakin da ta fitar ketare a yankin masana'antun da Sin ta gina
2018-12-27 09:40:11 cri

Kasar Habasha ta samu kudin shiga da ya kai dalar Amurka miliyan 38 na kayayyakin da ta fitar kasashen ketare daga yankin masana'antun da kasar Sin ta gina a kasar wato Hawassa industrial park a cikin shekaru biyun da suka gabata, wani jami'in kasar Habashan ne ya bayyana haka a jiya Laraba.

Yankin masana'antun na Hawassa wanda kamfanin CCECC ya gina, yana yankin kudancin kasar Habasha, an kammala aikin gina shi cikin watanni 9 a watan Yulin shekarar 2016.

CCECC ya kuma gudanar da aikin ginawa tare da kaddamar da aikin wasu yankunan masana'antu na Kombolocha da Adama, kana an cimma nasarar kashi 70 bisa 100 na aikin gina yankin masana'antu na Bahir Dar.

Da yake jawabi ga manema labarai, Mekonen Hailu, daraktan hulda da jama'a na hukumar zuba jarin kasar Habasha (EIC), ya ce an samu kudaden shiga na dala miliyan 38 ne daga nau'in tufafi wadanda aka samar da su daga wasu masana'antu cikin gida da na waje guda 20 dake yankin masana'antu na Hawassa.

Hailu ya kara da cewa, Hawassa ya samar da guraben ayyuka kimanin 23,000 ga 'yan kasar Habasha, inda kuma suke kara samun horo game da yadda za su kara inganta ayyukansu.

Habasha tana fatan gina yankunan masana'antu kimanin guda 30 nan da shekarar 2025, a kokarin da take yi na zama cibiyar masana'antu kuma kasa mai matsakaicin ci gaban tattalin arziki.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China