in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bikin al'adun Sinawa don murnar bikin bazara a Habasha
2019-01-20 15:27:33 cri

Da yammacin ranar Juma'a aka gudanar da kasaitaccen bikin nuna ala'dun Sinawa a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, don murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin dake tafe.

'Yan wasan fasaha na jihar Mongolia ta gida ta kasar Sin sun yi wasan kundunbala, sun rera wakoki, da kuma yin raye rayen na kananan kabilun kasar, bikin ya samu halartar dandazon mutane da suka hada da Sinawa dake zaune a Addis Ababa, da kuma 'yan kasar ta Habasha.

Da yake jawabi ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Yang Ying, daraktan kwalejin Confucius dake jami'ar Addis Ababa ya ce, bikin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin shi ne biki mafi muhimmanci a kasar Sin wanda ke tattara iyalai Sinawa da abokan arziki waje guda don samun nishadi da farin ciki da juna.

Genet Dagnchew, wata mace da ta halarci bikin daga kasar Habasha, ta ce bikin gargajiyar zai kara karfafa dankon zumuncin dake tsakanin Habasha da Sin.

Ta ce bikin gargajiyar da ta halarta ya ba ta damar yin tunanin zuwa kasar Sin domin kara samun fahimta game da al'adun Sinawa da yanayin zamantakewar rayuwarsu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China