in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta yi Allah wadai da harin da aka kai a asabitin Benghazin Libya
2018-12-27 09:53:24 cri

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi Allah wadai da harin da 'yan bindiga suka kaddamar kan wani asibiti dake birnin Benghazi na gabashin kasar Libyan.

"WHO ta yi Allah wadai da babbar murya game da kai harin wanda ya faru a ranar 26 ga watan Disamba a asibitin Al Jala dake Benghazi, wanda ya yi matukar tayar da hankalin marasa lafiya, da ma'aikatan lafiyar, kana ya lalata wasu muhimman kayayyakin asibitin," in ji hukumar ta WHO.

Hukumar lafiyar ta bukaci dukkan bangarori da su mutunta dokokin hakkin dan adam na kasa da kasa, kuma su kiyaye lafiyar jami'an lafiyar da kayayyakin kiwon lafiya a asibitocin."

Bayan da aka hana su damar shiga asibitin, wasu gungun 'yan bindigar sun haifar da rudani a lokacin da suka bude wuta a wani sashin ba da kulawar gaggawa na asibitin, in ji hukumar gudanarwar asibitin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China