in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano makeken kabarin wadanda mayakan IS suka hallaka a Sirte na Libya
2018-12-25 09:23:35 cri

Ministan harkokin cikin gidan kasar Libya ya sanar a jiya Litinin cewa, an gano wani makeken kabari wanda ke dauke da gawarwakin mutane da aka yi amanna mabiya addinin Kirista ne 'yan kasar Habasha wadanda mayaka masu da'awar kafa daular Islama na IS suka hallaka su a birnin Sirte a shekarar 2015.

A wata sanarwa daga sashen binciken munanan laifuka na ma'aikatar, ta ce, an gano katon kabarin ne a lokacin da ake bincikar wasu mambobin kungiyar ta IS wadanda ake tsare da su.

"Kimanin gawarwakin mutane 34 ne aka gano, kuma an adana gawarwakin a wata cibiya da aka tanada. Za'a mika gawarwakin ga iyalan mutanen, da zarar hukumomin cikin gidan kasar da na kasa da kasa sun kammala dukkan shirye shiryen da suka dace." kamar yadda sashen binciken ya bayyana cikin wata sanarwa.

A ranar 19 ga watan Afrilun shekarar 2015, IS ta wallafa wani faifen bidiyo wanda ke nuna yadda mayakan 'yan ta'addan ke zartar da hukuncin kisa kan wasu gungun mutane bakaken fata wadanda suka bayyana su da cewa, mayakan kasar Habasha ne mabiya addinin Kirista.

Bidiyon ya nuna yadda mayakan suka dinga harbin mutanen a kawunansu a wani wuri dake kudancin Libya, yayin da wasu mayakan na IS kuma suka dinga yiwa wasu mutanen yankan rago a wani waje dake gabashin kasar Libya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China