in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai yiwuwar samun ci gaba a nahiyar Afrika a 2019
2019-01-29 14:30:36 cri

Wani rahoton hasashen ci gaban nahiyar Afrika a bana da aka kaddamar jiya a Johannesburg na Afrika ta kudu, ya ce akwai yiwuwar nahiyar ta samu ci gaba a fannonin tattalin arziki da shugabanci da muhallin kasuwanci.

Rahoton wanda Brahima Coulibaly, babban jami'i kuma daraktan shirin raya Afrika na cibiyar bincike ta Brookings ya kaddamar, na kunshe da babuka daban daban da manyan mutane da malamai da kungiyoyin al'umma suka rubuta.

Cikin wani babi da ya rubuta, shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya ce gudumuwar Afrika ta kudu ga raya nahiyar, za ta dogara ne ga yunkurinsu na kawo karshen shekaru 10 da aka shafe ba tare da samun ci gaban tattalin arziki ba.

Ya kara da cewa, yankin ciniki cikin 'yanci na Afrika, zai ba nahiyar damar cimma burinta na inganta cinikayya da bunkasa masana'antu da kuma dogaro da kai.

Yayin kaddamarwar, Brahima Coulibaly, ya ce kasashen Afrika ne za su mamaye kusan rabin kasashen da za su samu saurin ci gaban tattalin arziki a bana. Yana mai cewa, abubuwa daban daban dake akwai a nahiyar na samar da damarmakin zuba jari tare da jan hankali abokan hulda daga ketare. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China