in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sauya tsarin lura da shukar Cocoa zai taimakawa yammacin Afirka wajen dakile sare daji
2019-01-25 20:12:44 cri

Jami'in tsare tsare a cibiyar nazari game da raya noman Cocoa domin samar da ci gaba Richard Asare, ya ce tsarin inganta noman Cocoa na kasashe hudu dake yammacin Afirka, zai taimaka wajen dakile matsalar sare daji, da kaucewa matsalolin sauyin yanayi.

Richard Asare, ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na Xinhua a jiya Alhamis, cewa shuka Cocoa a kasashen yammacin Afirka, ya samar da tsarin aiwatar da manufofin hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da sassan masu zaman kan su ko a PPP a takaice, lamarin da zai rage yawan sare daji domin samar da filayen noman cocoa.

Masanin ya yi tsokacin ne, yayin da ake tsaka da taron masana game da nazarin noman Cocoa. Ya ce yana da kwarin gwiwar cewa, ayyukan MDD masu nasaba da hakan, za su taimaka a tsawon lokaci wajen taimakawa manoma a kasashen Ghana, da Cote d'Ivoire, da Kamaru da Najeriya, ta yadda za su samu karin amfanin gona, da kuma ba da damar kare dazuka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China