in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandan Afrika ta kudu sun kama direbobin tasi 10 bayan arangama
2019-01-28 10:31:52 cri

Yan sandan kasar Afrika ta kudu a ranar Lahadi sun kama wasu direbobin motocin haya su 10, kana sun kwace wasu makamai bayan dauki-ba-dadin da suka yi sakamakon takaddama da ta kaure game da batun wasu hanyoyin mota a kasar.

Yan sandan sun ce, ana ci gaba da takun saka ne da direbobin motocin tasin tun a watan Disambar bara game da takaddama kan wasu hanyoyin mota a Mopani, dake lardin Limpopo.

A ranar Juma'ar da ta gabata kungiyar direbobin tasi ta dauki hayar wasu motocin jami'an tsaro wadanda ke rufa musu baya don gudanar da aikinsu a yankin da ake tababa kansa. Daga bisani, wata kungiyar mutanen da aka yi amanna masu adawa da kungiyar dirobobin ne suka afkawa jami'an tsaron da aka dauko hayar tasu,

Daga bisani mutanen dake cikin motocin jami'an tsaro suka mayar da martani ta hanyar harbe harbe kan motocin tasin.

"Mutane uku sun samu raunukan a sanadiyyar alburusan da suka same su kuma sun ji munanan raunuka,"in ji kakakin 'yan sandan lardin Limpopo Moatshe Ngoepe, ya kara da cewa, ana ci gaba da tsare mutane 10 bayan an kama motar da suke cikinta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China