in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin a Lebanon ya gudanar da bikin murnar sabuwar shekarar Sinawa da jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD
2019-01-28 13:40:13 cri

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Lebanon, ya gudanar da biki a ranar Asabar tare da jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD, domin murnar sabuwar shekarar Sinawa

Sama da mutane 200, ciki har da jakadan kasar Sin a Lebanon, Wang Kejian da shugaban shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Lebanon (UNIFIL) Stefano Del Col da 'yan siyasa da jami'an sojin Lebanon ne suka halarci bikin.

Wang Kejian, ya jadadda muhimmiyar rawar da UNIFIL ya taka wajen wanzar da zaman lafiya a kudancin Lebanon.

Ya kuma yabawa kokarin dukkan dakarun wanzar da zaman lafiya na UNIFIL, ciki har da Sinawa, wadanda ya ce sun rabu da kasashe da masoyansu, suna iyakar kokarin tabbatar da zaman lafiya a wata kasa karkashin rantsuwar MDD ta tabbatar da zaman lafiya a duniya.

A nasa bangaren Stefano Del Col, ya ce tawagar sojoji Sinawa, wani muhimmin bangare ne na UNIFIL tun daga shekarar 2006

Ya kuma yi kira ga dukkan dakarun da su guudanar da aikinsu bisa sadaukarwa, domin cimma burin UNIFIL. Ya kuma bukaci su gudanar da aikinsu bisa hadin gwiwar gwamnatin Lebanon da rundunar sojinta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China