Sai dai kuma, shugaba Michel Aoun na Lebanon bai amince da murabus din da Hariri ya yi ba, a ganinsa hakan ya sabawa doka, domin ba a gabatar masa da takardar yin murabus din a kasar Lebanon ba.
Haka kuma, shugaba Aoun yana cewa ,kasar Saudiyya ce ta tilastawa Hariri ya yi murabus, sannan aka yi masa daurin talala, don haka Lebanon take zargin masarautar Saudiya ta neman ta takalar fada.
A jiya ne Hariri ya ziyarci kasar Masar daga birnin Paris, inda ya tattaunawa da shugaba Abdel Fatah Sissi, kana daga bisani ya kai ziyarar ba za ta kasar Cyprus inda nan ma ya tattaunawa da shugaba Nicos Anastasiades.(Ibrahim)