A cewar sanarwar, Aboul Gheit ya gana da Hariri, kuma ana ganin cewa wannan ganawar tana da babbar ma'ana, kana sun yi shawarwari a tsakaninsu kuma sun amince za su gana a helkwatar kungiyar gamayyar kasashen larabawa a lokacin da Haririn ya ziyarci birnin Cairo na kasar Masar.
A ranar Litinin, Aboul Gheit ya bayyana cewa, Lebanon ba zata taba kasancewa a matsayin wani dandalin yaki tsakanin kasar Iran da kasashen larabawa ba, bayan wata ganawar ta daban da yayi da shugaban kasar Lebanon Michel Aoun da kuma kakakin majalisar dokokin kasar Nabih Berri.
Ministocin harkokin wajen kasashen mambobin kungiyar ta Arab League, sun yi wani taro a farkon wannan mako inda suka yi Allah wadai da Iran da kuma kungiyar Hezbollah, inda suka zargesu da wargaza zaman lafiyar yankin, kuma sun sha alwashin gabatar da wannan batu gaban kwamitin tsaron MDD.(Ahmad Fagam)