in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afirka ta kudu ya kafa kwamitin kwararru domin shawo kan kalubalen makamashin lantarki
2018-12-15 16:20:48 cri

Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya kafa wani kwamitin kwararru na musamman, wanda zai maida hankali ga zakulo hanyoyin dakile matsalar da al'ummar kasar ke fuskanta sama da wata guda, a fannin hidimar samar da lantarki.

Kwamitin da aka nada domin nazartar ayyukan kamfanin Eskom na wutar lantarkin kasar, zai samar da shawarwari ga gwamnati, wadanda za su ba da damar warware kalubalen sassan ba da hidimar biyan kudi, da tsarin gudanarwa, da na tattara kudade da kamfanin ke fuskanta.

Shugaban Afirka ta kudun ya ce, kwamitin da ya kafa, ya kunshi masana da gogaggu a fannin makamashin lantarki, da bangaren jagorancin ayyukan samar da lantarkin, da kwararru a fannin tattalin arziki.

Ayyukan da aka dorawa kwamitin sun kuma kunshi gano hanyoyin sake fasalin ba da hidimar lantarki a kasar bisa sauye sauyen da ake samu a bangaren, wadanda suka kunshi amfani da sabbin fasahohi, da dabarun sauke tulin bashin dake kan kamfanin na Eskom.

Mr. Ramaphosa ya kara da cewa, daukar wannan mataki ya wajaba, duba da yadda karancin lantarki ke haifar da koma baya ga tattalin arzikin al'ummar kasar. Ya ce, akwai bukatar samar da mafiya, karkashin tsare tsare masu cin gajere, da matsakaici, da dogon zango a wannan fanni.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China