in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya jagoranci taro na shida na kwamitin tsakiya game da zurfafa gyare gyare
2019-01-23 20:07:32 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taro na shida, na kwamitin tsakiya na JKS game da zurfafa gyare gyare a kasar.

Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban hukumar gudanarwa ta rundunar sojojin kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli, na hukumar dake lura da aiwatar da matakan zurfafa gyare gyare ta kasar, ya shugabanci taron ne a yau Laraba.

A cikin jawabin sa, shugaban ya yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki, da su tabbatar da ganin an cimma nasarori na hakika, a muhimman sassa masu muhimmanci, da kudurori dake hadewa da ajandar shekarar 2020.

Shugaba Xi ya ce, ya dace kasar Sin ta ci gaba da yakin da take yi da kalubale masu hana ruwa gudu, da kau da dukkanin matsaloli masu tsanani, a kuma tabbatar nasarori a dukkanin manufofin da aka sanya gaba. Kaza lika a kuma kafa wani ginshiki na aiwatar da gyare gyare, kamar yadda hakan ke tsare cikin kundin zama na uku, na taro na 18 da kwamitin kolin JKS ya gabatar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China