in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya bukaci daukar matakan kare manyan hadurra domin wanzar da tattalin arziki mai nagarta
2019-01-21 20:07:32 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci manyan jami'an gwamnati, da su dauki matakan da suka wajaba, na kare aukuwar manyan hadurra, da ka iya haifar da illa ga kyakkyawan yanayin tattalin arzikin kasa, tare da wanzar da managarcin yanayi na zamantakewar al'umma.

Shugaba Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, ya yi wannan kira ne a Litinin din nan, cikin jawabin sa na bude taron nazari, na kwalejin horaswa ta kwamitin kolin JKS, wanda manyan jami'an jam'iyyar daga larduna daban daban, da jami'ai daga ma'aikatun kasar suka halarta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China