in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya sa hannu kan kudurin kawo karshen rufe hukumomin gwamnatin kasar na wucin gadi
2019-01-26 16:25:20 cri

Da yammacin jiya Juma'a gwamnatin Amurka ta sake bude hukumomin kasar bayan da shugaban kasar Amurkan Donald Trump ya rattaba hannu kan kudurin samar da kudaden da za'a biya hukumomin har tsawon makonni 3.

Sanarwar da fadar White House ta fitar, ta ce shugaba Trump ya sanya hannu kan dokar samar da karin kudi a cikin kasafin kudin kasar na shekarar 2019, wanda ya kunshi samar da kudaden da za'a baiwa hukumomin kasar har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu.

Daga cikin abubuwan da aka tsame cikin kudirin dokar, ba a ambaci batun gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico, wanda shugaba Trump ya tsaya kai da fata don neman majalisar dokokin kasar ta sahhale masa ba. Sai dai fadar ta White House da jam'iyyar Democrats za su ci gaba da neman sasantawa da juna game da batun tsaro kan iyakar kasar mai cike da sarkakiya nan da makonni 3 masu zuwa.

Sai dai yin watsi da bukatar shugaban Amurkan, babban koma baya ne ga fadar ta White House, kasancewar batun tsaro kan iyakar kasar da Mexico shi ne babban batu da ya mamaye alkawurran gangamin yakin neman zaben mista Trump.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China