in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantaka tsakanin Sin da Amurka ta ba da gudunmowa ga zaman lafiya da ci gaban duniya
2019-01-20 16:21:34 cri

Wani babban jami'in diplomasiyyar kasar Sin ya fada cewa, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ta haifar da manyan nasarori cikin shekaru 40 da suka gabata, inda ta samar da babbar moriya ga al'ummomin kasashen biyu, da kuma ba da gagarumar gudunmowa ga zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.

Da yake jawabi a taron bikin murnar cika shekaru 40 da kafa huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka, jakadan Sin, Wang Donghua, ya ce tsoffin magabatan shugabanin kasashen Sin da Amurka su ne suka kafa tarihin kulla dangantaka tsakanin kasashen biyu, bisa tushen hikima da hangen nesa ta fuskar siyasa don kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Magajin birnin San Francisco, London Breed, ta fada a lokacin bikin cika shekaru 40 da kulla huldar dipolamasiyyar Sin da Amurka cewa, an samu karuwar musaya da fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.

Ta ce an samu manyan damammakin yin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, kuma wannan biki wata dama ce da bangarorin biyu za su kara tunawa da irin nasarorin da suka cimma a tsakaninsu.

"A wannan yanayin da duniya ke kara dunkulewa waje guda, kasashen duniya za su samu makoma mai kyau ne idan suka yi aiki tare a matsayin tsintsiya madaurin ki daya," in ji Breed.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China