in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump: Ana samun karuwar matsalar jin kai a kan iyakar Amurka da Mexico
2019-01-09 15:04:28 cri

Shugaba Trump na kasar Amurka ya yi ikirarin cewa, ana samun karuwar matsalar jin kai a kan iyakar Amurkar da Mexico. Shugaba Trump ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi da ya yi wa al'ummar kasar ta kafar talabijin a daren jiya Talata, a gabar da ake tayar da jijiyar wuya tsakaninsa da majalisun dokokin kasar na neman sama da dala biliyan biyar da ya bukata don gina katanga tsakanin Amurkar da kasar Mexico. Takaddamar da ta haifar da rufe wasu sassa da hukumomin tarayyar Amurka, kwanaki 18 a jere.

Amma kuma da kammala jawabin na Trump, sai kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi da shugaban majalisar dattawan kasar Chuck Schumer, suka mayar da martani, inda suka zargi shugaba Trump da haddasa rikici, kana suka bukace shi da ya bude ma'aikatun gwamnatin da aka rufe. Shugaba Trump dai yana zargin 'yan kasar ta Mexico ne da safarar miyagun kwayoyi da ma shiga kasar ta Amurka ba bisa ka'ida ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China