in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta bayyana barazanar Amurka kan kasar Sin a matsayin raha
2019-01-21 20:37:54 cri

Wani jami'in kasar Isra'ila ya ce, gargadin da Amurka ke yi game da cudanyar cinikayya tsakanin Sin da kasar sa wasan yara ne kawai.

Wani rahoto daga Amurka, ya bayyana damuwar da wasu jami'an kasar suka nuna, game da jarin da kasar Sin ke zubawa a Isra'ila, musamman ma a tashar jiragen ruwa ta Haifa, matakin da jami'an na Amurka ke cewa, ka iya baiwa Sin damar yin leken asiri, da satar bayanai ta yanar gizo.

To sai dai kuma, wani jami'in gwamnatin Isra'ila da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce batun a ce Sin na da burin yin leken asiri ma bai taso ba, jami'in ya ce, idan Sin na bukatar tattara bayanan sirri, gida za ta kama a Haifa ta sanya na'urori, amma ba wai zuba jari domin mallakar wani sashe na tashar ruwan dake yankin ba.

Da take tsokaci game da hakan, yayin taron manema labarai na yau, mai magana da yawun ma'ikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce ko kawayen Amurka ma na daukar wancan zargi a matsayin raha, shin ko akwai bukatar ma Sin ta maida wani martani na daban?

Ta ce Amurka na yawan amfani da kalmar tsaron kasa, domin ambata halastattun harkoki na cinikayyar kamfanonin Sin, kana tana kuma yawan kaucewa hakikanin gaskiya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China