Babban sakataren ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya dake gudana yanzu haka a Davos. Ya kara da cewa, yanzu duniya na fuskantar barazanar cinikayya, matsalar bashi, rashin daidaiton kasuwar kudi da sauran hadurra, amma sauyin yanayi ya fi tsanani bisa hasashen da masana suka yi. (Bilkisu)