in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron sauyin yanayi na San Francisco
2018-09-14 11:17:00 cri
An bude taron masu ruwa da tsaki, game da sauyin yanayi na birnin San Francisco dake kasar Amurka. Taron na kasa da kasa wanda aka bude a ranar Alhamis, ya hallara wakilan gwamnatocin yankuna, da na jami'an masana'antu, da cibiyoyin bincike. Ana kuma sa ran za su shawarta game da matakan dakile mummunan tasirin da sauyin yanayi ke haifarwa ga duniya.

A jawabin ta yayin bikin bude taron, mai rike da mukamin magajin garin birnin San Francisco uwargida London Breed, ta yi kira ga kasashen duniya da su hada karfi da karfe, wajen tunkarar kalubalen sauyin yanayi.

Shi kuwa a nasa jawabin, wakilin musamman na kasar Sin game da sauyin yanayi Xie Zhenhua, cewa ya yi, Sin na daukar yaki da sauyin yanayi a matsayin muhimmin mataki na raya tattalin arziki, da bunkasa zamantakewar al'ummar ta.

Ya ce Sin ta samu ci gaban alkaluman GDP da kaso 1.5, tsakanin shekarun 2005 zuwa 2017, amma duk da haka ta yi nasarar rage hayaki mai gurbata muhalli nau'in carbon da ake fitarwa a sassan kasar da kaso 46 bisa dari, matakin da ya haura burin da ake da shi na rage kaso 40 zuwa 45 bisa dari, na nau'oin wannan hayaki nan da shekara ta 2020.

Mr. Xie ya kara da cewa, a bana, kasar Sin ta zuba jarin dalar Amurka biliyan 126.7 wajen samar da makamashi mai tsafta, wanda hakan ya sanya ta zama kasa ta daya a duniya cikin shekaru 6 a jere, wadda ta dara saura a wannan fani.

Taron na birnin San Francisco, ya samu halartar wakilai sama da 4,000 daga sassan nahiyoyin duniya 6. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China