in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar taron MDD ta yi fatan samun cikakken sakamako yayin taron birnin Katowice
2018-11-22 12:43:25 cri
Shugabar babban taron MDD ta wannan karo Maria Fernanda Espinosa, ta yi fatan samun cikakken sakamako, a yayin taron sauyin yanayi da zai gudana a birnin Katowice na kasar Poland.

Espinosa ta bayyana hakan ne ga manema labarai a jiya Laraba, a hedkwatar MDD dake birnin New York, tana mai cewa, fatan da ake da shi shi ne, fidda shirye shirye masu nagarta, ko da yake za a bukaci kwazo, da maida hankali, da yarda da juna, yayin da ake tattaunawa.

Jami'ar za ta isa birnin Katowice, domin halartar taron na sauyin yanayi, kuma tuni ta bayyana batun sauyin yanayin, a matsayin lamari dake matukar bukatar kulawa daga dukkanin sassa. Ta ce akwai bukatar karkata ga raya tattalin arziki ta hanyoyin amfani da fasahohi da ba za su rika gurbata muhalli ba, wadanda za su zamo masu fa'ida ga cigaban da ake fata. (Saminu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China