in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Za a kira taron kasashe biyar masu amfani da makaman nukiliya a Beijing
2019-01-24 20:25:32 cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, bisa matsayinta na mai sulhuntawa ta karba karba a tsarin kasashe biyar masu amfani da makaman nukiliya, kasar Sin za ta kira taron kasashen biyar a hukumance a nan birnin Beijing a ranar 30 ga wata.

Hua Chunying ta kara da cewa, bisa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, kasashe biyar wato kasar Sin da Amurka, da Rasha, da Birtaniya, da Faransa, suna iya amfani da makaman nukiliya. A cikin shekarun baya bayan nan, kasashen biyar suna sulhuntawa tsakaninsu lami lafiya, kuma wannan ne karo na farko da za su kira taro a hukumance, inda yanzu suke kokarin gudanar da aikin share fage, domin halartar taron da za a kira a Beijing. Ta ce ko shakka babu hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyar, yana da babbar ma'ana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China