in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na kara taka rawa wajen hana yaduwar makaman nukiliya
2017-12-22 15:12:01 cri

Sakataren zartaswa na kwamitin share fage ta kungiyar hana gwajin makaman nukiliya Lassina Zerbo, ya ce kokarin da kasar Sin take wajen kafa tasoshin sa ido kan gwajin makaman nukiliya ya nuna cewa, kasar ta cika alkawarin da ta dauka game da hana yaduwar makaman nukiliya a fadin duniya, inda ya ce tana kara taka rawar gani a fannin.

An kammala aikin gina tashar sa ido kan gwajin makaman nukiliya ta farko a kasar Sin ne a watan Disamban bara, kuma ya zuwa yanzu wato karshen shekarar bana, adadin tasoshin sa ido kan gwajin makaman nukiliya da aka kafa a kasar ya kai biyar.

Da yake ganawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Lassina Zerbo ya ce, aikin na da ma'anar tarihi, kana ya jaddada cewa, kasar Sin kasa ce mai tasowa, wadda ta zama abun koyi ga sauran kasashe masu tasowa wajen shiga harkokin kasa da kasa dake karkashen tsare-tsaren MDD, har tana ba da mamaki a fannoni daban daban ga al'ummun kasashen duniya ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China