Yau Litinin kasar Amurka ta maido da takunkumin da ta kakabawa kasar Iran a fannonin makamashi da harkar kudi, wannan shi ne karo na biyu da Amurka ta dauki matakin kan Iran tun bayan da ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, an daddale yarjejeniyar nukiliyar Iran ne karkashin amincewar kwamitin sulhun MDD, kamata ya yi a aiwatar da ita daga dukkan fannnoni, a don haka kasar Sin tana fatan sassan da abin ya shafa su yi hangen nesa su yi hakuri har su dauki matakin da ya dace.
Jami'ar ta yi wannan tsokaci ne yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing.(Jamila)