Mr. Lavrov ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da takwaransa na kasar Jordan Ayman Safadi a birnin Sochi na kasar Rasha, yana mai cewa, idan kasar Amurka ta fice daga yarjejeniyar, kamar yadda shugaban kasar Donald Trump ya jaddada, gamayyar kasa da kasa za su rasa wata muhimmiyar yarjejeniya game da hana yaduwar makaman nukiliya a duniya.
Bugu da kari, ya ce, mai yiyuwa ne, takardun da Isra'ila ta gabatar a kwanan baya game da batun nukiliyar kasar Iran tsoffi ne, saboda a halin yanzu hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa na sa-ido kan dukkan ayyukan da suka shafi nukiliyar kasar Iran.
A daren ranar 30 ga watan Afrilu da ya gabata ne, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya shaidawa taron maneman labarai cewa, hukumar leken asirin Isra'ila ta samu wasu takardu na sirri daga kasar Iran, inda take zargin kasar Iran da ci gaba da shirinta na kera makaman nukiliya, sabanin yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da aka kulla. (Maryam)