Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya nada Xia Huang, tsohon jakadan kasar Sin dake wakilci a kasar jamhuriyar Congo a matsayin manzon sa na musamman kan batun yankin manyan tafkunan Afirka.
A Larabar nan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta yi maraba da nadin, ta kuma jaddada cewa, Xia Huang zai yi kokari matuka a aikin ingiza zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma ci gaba a yankin manyan tafkunan Afirka karkashin goyon bayan MDD, kuma ita ma kasar Sin, za ta ci gaba da goyon bayan kokarin babban sakataren MDD da kuma jakadan Xia. (Jamila)