in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta sa kaimi kan aikin kwamitin sulhun MDD domin daidaita rikicin shiyya shiyya
2018-10-31 18:55:01 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, kasarsa za ta jagoranci kwamitin sulhun MDD a hukumance, daga ranar 1 ga watan Nuwamban dake tafe, kuma yanzu haka tana tattaunawa da sauran kasashen mambobin kwamitin, kan shirin aikin majalissar na watan Nuwamba.

Lu Kang ya ce hakan zai sa kaimi ga aikin kwamitin, domin kara samun ci gaba a fannin warware rikicin shiyya shiyya a siyasance, kuma yadda ya kamata. Jami'in ya yi wannan tsokaci ne a Larabar nan, yayin taron ganawa da manema labarai da aka saba yi a nan birnin Beijing.

Ya ce bisa shirin da aka tsara, kwamitin sulhun MDD, zai kira taruka sau da dama, domin yin nazari kan batutuwan dake shafar yanayin da kasashen Syria, da Libya, da Iraki, da Lebanon, da yankin Gabas ta Tsakiya, da Bosnia Herzegovina, da yankin Sahel na Afirka ke ciki.

Ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta kara karfafa cudanya, dake tsakaninta da kasashen da ba mambobin kwamitin sulhu ba, musamman ma kasashen da batutuwan tashe tashen hankula suke shafa, domin gudanar da aikinta a kwamitin ba tare da wata rufa rufa ba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China