Xi Jinping ya jaddada cewa, bana aka cika shekaru 70 da kulla huldar jakadanci tsakanin Sin da Koriya ta Arewa, kuma yana fatan yin kokari tare da Kim Jong-un don ciyar da dangantakar kasashen biyu gaba.
A nasa bangaren, Kim Jong-un ya ce, yana fatan amfani da ziyararsa a Beijing a wannan karo don karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu, da yin musayar ra'ayi kan karfafa hadin-gwiwarsu, a wani kokari na daukaka ci gaban huldar kasashen biyu.
Har wa yau, bangarorin biyu sun bayyana cewa, za su nuna himma da kwazo wajen daidaita matsalar zirin Koriya ta hanyar siyasa, da kara samar da alfanu ga jama'ar kasashen Sin da Koriya ta Arewa, tare kuma da bayar da gudummawa ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali da samar da bunkasuwa a wannan shiyya da ma duk fadin duniya baki daya.(Murtala Zhang)