Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin tsakiyar jamiyyar kwaminis (CPC) ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin tsakiyar rundunar sojojin kasar, ya bada umarnin ne a cikin wani jawabin da ya gabatar a babban taron kwamitocin siyasa da na shari'a wanda aka gudanar a birnin Beijing a ranakun Talata da Laraba.
Ya umarci hukumomin tabbatar da doka da na shari'a da su kara kaimi, su daidaita ayyukansu kana su inganta kwarewar aikinsu. (Ahmad Fagam)