in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila za ta ci gaba da yunkurin fatattakar Iran dake Syria
2018-06-18 16:07:35 cri

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi gargadin cewa, Isra'ila za ta ci gaba da daukar dukkan matakai kan Iran da kawayenta dake Syria domin hana su kafa sansanin soji a yankin arewacin kasar wanda ke makwabtaka da Isra'ilar.

Ya yi wannan gargadi ne a lokacin taron majalisar ministocin kasar na mako mako a birnin Jerusalem.

Netanyahu ya shedawa majalisar ministocin kasar cewa, tuni ya tattauna wannan batu da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da kuma sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo a karshen mako.

Ya ce, yana jaddada matsayin kasarsa game da batun Syria. Da farko, ya kamata Iran ta janye daga Syria dugurungum. Na biyu, za su dauki mataki, kuma tuni ma sun fara daukar matakai game da duk wani yunkurin da Iran din da masu taimaka mata ke yi na kafa sansanin soji a Syriar.

Dama dai tuni Isra'ilar ta kaddamar da munanan hare hare ta jiragen sama a Syria, tana mai cewa, ta kaddamar da hare haren ne da nufin tarwatsa yunkurin Iran na kafa sansanin soji a Syria da kuma lalata dukkan makaman mayakan kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon wadanda ke samun goyon bayan Iran.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China