in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta kaddamar da hari a sansanin sojin Syria dake Aleppo
2018-07-16 11:16:03 cri

Kamfanin dillancin labarai na SANA ya rawaito cewa, a jiya Lahadi Isra'ila ta kaddamar da harin makamai masu linzami kan sansanin sojojin kasar Syria dake arewacin lardin Aleppo.

Rahotanni sun ce, makamai masu linzamin da Isra'ilan ta harba ya lalata sansanin sojojin sama na arewacin yankin al-Nayrab, kana harin ya yi barna mai yawa.

Harin da Isra'ilan ta kaddamar ya kasance a matsayin martani dangane da irin ci gaban da aka samu na ayyukan soji a kudanci, inda dakarun sojojin Syria suka yi nasarar kwace ikon lardin Daraa na kudancin Syria, ciki har da yankunan dake karkashin ikon 'yan tawaye dake kusa da yankunan da Isra'ilan ta mamaye.

Harin dai shi ne na baya bayan nan daga cikin jerin hare hare ta jiragen sama da kuma makamai masu linzami da aka kaddamar wanda Isra'ilan ta kaddamar kan sansanin sojojin Syria.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China