in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin zai ci gaba da karuwa cikin sauri, in ji Lin Yifu
2019-01-12 16:27:33 cri
Kwanan baya, tsohon babban masanin tattalin arzikin bankin duniya, kana shehun malamin jami'ar Peking Lin Yifu ya bayyana a birnin New York cewa, bisa hasashen da aka yi, an ce, adadin karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai kashi 6.5% a shekarar 2019, wanda zai bada gudummawa na kimanin kashi 30% ga karuwar tattalin arzikin duniya.

Cikin taron dandalin tattaunawar harkokin tattalin arzikin Sin na shekarar 2019 da aka yi a birnin New York na kasar Amurka a ranar 10 ga wata, Lin Yifu ya bayyana cewa, bayan kasar Sin ta fara aiwatar da matakan yin kwaskwarima a fannin tattalin arziki, wadanda suka hada da rage kayayyakin da aka samar fiye da kima, da rage yawan kayayyakin da aka adana da dai sauransu, Sin ta fara mai da hankali kan rage kudaden gudanarwar ayyukan kamfanoni da kuma kawar da matsin lambar da aka yiwa kamfanonin kasar wajen gudanar da ayyukansu, lamarin da zai taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin Sin. haka kuma, ya ce, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka kwanan baya, kamar su, rage harajin kamfanoni, kara saukin neman iznin gudanarwar ayyuka da dai sauransu, zasu ba da gudummawa wajen kafa yanayi mai kyau wajen gudanar da harkokin kasuwanci. A sa'i daya kuma, kasar Sin ta samarwa kamfanonin ketare karin damammaki wajen zuba jari a kasar Sin ta hanyar inganta ayyukan gina yankunan ciniki cikin 'yanci a kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China