in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Ya kamata Sin da Amurka su shawo kan bambancin dake tsakaninsu bisa tattaunawa
2018-08-04 15:49:44 cri

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce ya kamata kasashen Sin da Amurka, su shawo kan takaddamar dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.

Wang Yi ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da takwaransa na Amurka Mike Pompeo, a gefen taron ministocin harkokin wajen mambobin kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya.

Ya ce, hadin kai shi ne kadai abun da ya dace da Amurka da Sin, kuma shi ne abun da daukacin al'ummomin duniya ke sa ran gani. Yana mai cewa, yin fito-na-fito zai kara haifar da asara ne da zai yi tarnaki ga zaman lafiya da ci gaban duniya.

Ya kara da cewa, ya kamata bangarorin biyu su magance bambancin dake tsakaninsu tare da warware matsalarsu ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna bisa mutunci da adalci, ta yadda zai jagoranci dangantakarsu zuwa tafarkin da ya dace.

A nasa bangaren, Mike Pompeo, ya ce dangantakar Amurka da kasar Sin na da muhimmanci matuka, yana mai cewa, Amurka na sa ran dukkan kasashen biyu za su cimma nasara, kuma ba ta da niyyar yi wa ci gaban kasar Sin karan tsaye. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China