in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mamban majalisar zartaswar Sin Yang Jiechi ya kai ziyara Amurka
2018-02-11 12:03:35 cri

Mamba a majalisar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi ya kai ziyara kasar Amurka tsakanin renakun 8 zuwa 9 ga wannan wata, kan wannan batu, a jiya Asabar 10 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a birnin Washington na kasar ta Amurka cewa, ziyarar ta Yang Jiechi ta kasance ganawar kai tsaye karo na farko a tsakanin manyan jami'an kasashen biyu wato Sin da Amurka, tun bayan da shugabannin kasashen biyu suka yi ganawa a watan Nuwamban shekarar bara da ta gabata a nan birnin Bejing, ana sa ran ziyarar za ta taka rawa wajen tabbatar da sakamakon da aka samu yayin ganawar shugabannin kasashen biyu a Beijing, tare kuma da sa kaimi kan cudanya da hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu.

An ce, yayin ziyarar da ya yi, gaba daya sassan biyu wato Sin da Amurka suna ganin cewa, suna gudanar da huldar dake tsakaninsu yadda ya kamata a cikin shekarar 2017 da ta wuce, haka kuma sassan biyu sun amince da cewa, kamata ya yi su ci gaba da sanya kokari tare domin tabbatar da sakamakon da suka samu yayin ganawar Beijing. Inda mamban majalisar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi shi ma ya yi nuni da cewa, ya dace sassan biyu su kara gudanar da shawarwari dake tsakaninsu domin gudanar da hadin gwiwa daga dukkan fannoni, musamman ma wajen samar da makamashi da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya da sauransu, kana kamata ya yi sassan biyu su kara himmantuwa kan batun daidaita matsalolin da suke da su a fannin tattalin arziki da ciniki, ta yadda za su ciyar da huldar tattalin arziki da ciniki dake tsakaninsu lami lafiya.

A nata bangaren, gwamnatin Amurka ta bayyana cewa, ya kamata sassan biyu su yi kokari tare domin neman samun hanyar da ta dace, yayin da suke warware matsalolin da suka gamu da su wajen tattalin arziki da ciniki.

Game da batun makaman nukiliyar zirin Koriya kuwa, Yang Jiechi ya yi nuni da cewa, ya kamata kasashen duniya su nuna wa kasashen biyu wato Koriya da Kudu da ta Arewa goyon baya domin su kyautata huldar dake tsakaninsu, ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar ta Amurka bisa tushen amincewa da girmama juna, ta yadda za a daidaita matsalar ta zirin Koriyar yadda ya kamata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China