A jiya Talata da rana ne manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin firaministan kasar Liu He ya isa birnin Washington, don tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya da bangaren Amurka bisa gayyatar mahakuntan na Amurka.
Liu wanda har ila mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS shi ne yake jagorantar tawagar kasar Sin wadda ta kunshi mambobi daga manyan sassan tattalin arzikin kasar a wannan tattaunawa.(Ibrahim)