in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu zuba jari na Kenya da Sin sun hadu domin lalubo damarmakin zuba jari
2018-08-04 15:56:10 cri

Masu zuba jari na kasar Kenya da lardin Guangdong na kasar Sin, sun gudanar da wani taro jiya Juma'a a Nairobi, domin lalubo damarmakin zuba jari da za su taimakawa bunkasa manufofin ci gaban kasar.

Yayin taron, jami'an kasar Kenya, sun yi kira ga masu zuba jari daga Guangdong, da su kafa sana'o'i a kasar, wadanda za su mayar da hankali kan manufofin kasar na ci gaba, da ake wa lakabi da 'Manyan manufofi hudu' da suka shafi samar da gidaje masu rahusa da kiwon lafiya na bai daya da bunkasa masana'antu da kuma wadatuwar abinci.

A jawabinta na bude taron, babbar sakatariyar ma'aikatar kula da ciniki da masana'antu ta Kenya Betty Maina, ta ce manufofin za su taimakawa kasar samun gagarumin ci gaban tattalin arziki.

Ta kuma jadadda kudurin gwamnati na inganta hadin gwiwa da lardin Guangdong don samun moriyar juna karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya".

A nasa bangaren, babban manajan hukumar kula da zuba jari ta kasar Moses Ikiara, ya ce ba taimakawa masu zuba jari na Guandong wajen lalubo damarmakin zuba jari da abokan hulda na cikin gida kadai hukumar ta yi niyyar yi ba, har ma da samar musu da kyakkyawan yanayin saukaka harkoki kafin da bayan zuba jarin.

Shi kuwa jakadan kasar Sin a Kenya Sun Baohong, cewa ya yi, la'akari da Kenya a matsayin muhimmiyar abokiyar hulda, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin hada shawarar ziri daya da hanya daya da manufofin ci gaban kasar Kenya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China