in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta mara baya ga yunkurin farfado da ci gaban tattalin arziki bisa amfani da albarkatun ruwa
2018-11-27 10:04:10 cri

Gwamnatin kasar Sin, ta ce za ta mara baya ga kokarin kasashen duniya na inganta tattalin arziki bisa amfani da albarkatun ruwa, wanda ya dace da muradun ci gaba masu dorewa.

Wakilin kasar Sin na musammam game da harkokin nahiyar Afrika, Xu Jinghu, ya shaidawa taro kan dorewar tattalin arzikin albarkatun ruwa dake gudana a birnin Nairobin Kenya cewa, kasar Sin ta taimakawa kokarin al'ummomin duniya na bunkasa ci gaban tattalin arzikin albarkatun ruwa ta hanyar shugabanci na gari da yayata fasahohi da gogewarta na karfafa kiyaye muhallin albarkatun ruwa.

Xu Jinghu, ya ce kasar Sin na kira da a kulla kawance kan batun tare da zartar da kudurin da ya shafi batutuwan teku karkashin hadin gwiwar.

Kasar Kenya ce ke karban bakuncin taron kan tattalin arzikin albarkatun ruwa, wanda ya gudana karon farko a nahiyar Afrika, inda ya samu mahalarta sama da 10,000 daga kasashe 183.

Daga cikin mahalarta taron na yini 3, akwai sama da shugabannin kasashe da gwamnatoci 10 galibi na Afrika, da wakilan hukumomin kawance na kasa da kasa da na masana'antu da ministoci da masana kimiyya da kuma masu rajin kare albarkatun ruwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China