in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya sha alwashin hukunta masu yiwa kasarsa zagon kasa
2019-01-10 09:52:45 cri

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir a jiya Laraba ya bayyana cewa, wadanda ke yiwa kasarsa zagon kasa za su fuskanci hukunci mai tsanani kuma duk wani mataki na neman sauya shugabanci a kasar zai samu ne ta hanyar zabuka.

"Mutanen kasa su ne ke da alhakin tabbatar da shugabanci ta hanyar akwatunan zabe," al-Bashir ya furta hakan ne a lokacin da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa a Khartoum.

Ya kuma zargi wasu da bai bayyana sunansu ba da cewa, su ne ke shiryawa kasar Sudan makarkashiya da kuma yunkurin lalata ci gaban tattalin arzikin kasar.

Sai dai kuma shugaban na Sudan, ya yabawa wasu kasashen duniya aminai ga kasar wadanda ke tallafawa kasar ta Sudan da suka hada da kasashen Sin, Rasha, hadaddiyar daular Larabawa, da Qatar.

Bangarorin kasar Sudan masu neman shiga tsakani ta hanyar tattaunawar sulhu sun shirya wani gangami a ranar Laraba a babban dandalin taro na Green Square dake birnin Khartoum don nuna goyon baya ga gwamnatin al-Bashir.

Tun a ranar 19 ga watan Disambar shekarar 2018, yankunan kasar Sudan da dama, ciki har da Khartoum, suke fuskantar dandazon masu zanga zanga don nuna bacin ransa game da tabarbarewar yanayin tattalin arziki da tashin farashin kayayyakin masarufi a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China