in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu ta dawo da hakar mai a arewacin kasar
2019-01-09 13:00:12 cri

Ministan man fetur na kasar Sudan ta kudu Ezekiel Lol Gatkuoth ya bayyana cewa, kasarsa ta dawo da aikin hako mai a yankin arewacin Unity, bayan yakin tsawon shekaru biyar da ya kai ga lalata rijiyoyin man.

Ministan ya bayyana a ranar Litinin da ta gabata cewa, a ranar 31 ga watan Disambar shekarar da ta gabata ya ba umarnin gudanar da kashin farko na aikin hako mai a rijiyoyi 5 cikin rijiyoyi mai guda 16.

Ya bayyana cewa, shi da takwaransa na kasar Sudan Azhari A. Abdallah za su kaddamar da cikakken shirin hako mai a rijiyoyin mai dake Unity. Kasar Sudan ta kudu dai ta dogara ne ga aikin hako mai domin ta biya kusan kaso 98 cikin 100 na kudaden abubuwan da take son kashewa, duk da kokarin da mahukuntan kasar ke yi na kara yawan kudaden da take samu a bangaren da bai shafi albarkatun mai ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China