in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hankulla sun kwanta a dukkan jihohin Sudan
2018-12-27 09:16:19 cri

Yan sandan kasar Sudan sun sanar a jiya Laraba cewa, an samu farfadowar zaman lafiya a dukkan jihohin kasar bayan zanga zangar da ta barke a yankuna da dama na kasar don nuna adawa game da tabarbarewar yanayin tattalin arzkin kasar.

"Zaman lafiya ya farfado a dukkan jihohi," Hashim Abdel-Rahim, kakakin hukumar 'yan sandan kasar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

"Ba mu samu wani rahoton rikici ko zanga zanga ba a ranar Laraba," in ji shi, ya kara da cewa, "dukkannin jihohi sun samu cikakken zaman lafiya, ciki har da birnin Khartoum, 'yan sanda ba su kara samun wata hayaniya ba."

Sama da mako guda da ya gabata, yankuna da dama a kasar Sudan, ciki har da birnin Khartoum, sun sha fama da mummunar zanga zanga, inda mutane suke nuna bacin ransu dangane da tabarbarewar yanayin tattalin arzikin kasar da kuma tashin farashin kayayyakin bukatun yau da kullum.

A bisa alkaluman da gwamnati ta fitar, a kalla masu zanga zangar 8 ne aka kashe a jihar Gadarif dake yankin gabashin Sudan, da kuma birnin Atbara dake arewacin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China