A jiya Talata, shugaban babban bankin kasar Sin ko PBOC, Yi Gang, ya gana da wasu manema labarun kasar, don amsa tambayoyinsu, don gane da yadda bankin zai aiwatar da manufofin da aka tsara, a taron gwamnatin tsakiyar kasar Sin, don gane da aikin raya tattalin arziki.
An gudanar da ganawar ne dai a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar ta Sin.
A wajen ganawar, yayin da aka yi masa tambaya kan yadda za a taimakawa kamfanoni masu zaman kansu, gami da kananan kamfanoni, wajen samun rance, jami'in ya amsa da cewa, bankin PBOC zai aiwatar da wasu fasahohi masu alaka da manufofin kudi, don samar da isashen rance ga kananan kamfanoni masu bukata. A sa'i daya kuma, zai yi amfani da hanyoyin da suka hada da ba da rance, da takardun bashi, da hannayen jari, wajen taimakawa kamfanoni masu zaman kansu samun kudade. (Bello Wang)